Wednesday 28 January 2026 - 23:42
Tunanin Mahadawiyya da Intizar An Kafa Shi Ne Bisa Ruhin Juyin Juya Halin Musulunci

Hauza/ Shugaban hedkwatar fadada Mahadawiyya da Intizar ya bayyana cewa Mahadawiyya da Intizar ra'ayi ne mai bangarori da dama a ruhin juyin juya halin Musulunci, kuma ya kamata cibiyar fadada Mahadawiyya da Intizar su sake fito da wannan tunani.

A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, Ayatullah Alireza A'arafi a taron hedikwatar raya al'adu da raya al'adar Mahadawiyya karo na biyu da aka gudanar a dakin taro na masallacin Jamkaran ya bayyana cewa: "Muna matukar godiya kan dukkanin kokari da himmar da shugaban masallaci mai daraja na Jamkaran yake yi."

Da yake ishara da cewa tushen aikin wannan hedikwatar shi ne ka'idar da wannan majalisa da sakatariya ta amince da su, Shugaban makarantun Hauza ya ce: "Dole ne mu yi kokarin kafa hedkwatar Mahadawiyya a matsayin hedikwatar kasa mai aiki da cikakken ka'ida da tsarin da aka tsara tare da shigowar cibiyoyi daban-daban masu tasiri, aiki da ci gaba."

Shugaban hedikwatar raya al'adun Mahadawiyya da Intizar, yayin da yake bayyana cewa abin da muka ba da muhimmanci shi ne cewa ya zama wannan hedikwatar tana da cikakken tsari kan lamarin Mahadawiyya da Intizar, ya ce: Mahadawiyya da Intizar ra'ayi ne mai bangarori da dama a ruhin juyin juya halin Musulunci, kuma ya kamata wannan hedikwatar ta sake fito da wannan tunani."

Shugaban makarantun Hauza na kasa ya yi nuni da cewa, dukkan ayyukanmu ya kamata su kasance bisa dabaru da tsare-tsare, ya kuma ce: "Haka nan, ya kamata dukkan ayyukanmu su kasance daidai da hadafin shekaru biyar."

Ayatullah A'arafi, yayin jaddada cewa bayan ayyukan cibiyar, kar mu yi sakaci da ayyukan mutane ya ce: "Sashin karshe na ayyukanmu shi ne jama'a da jami'o'i da makarantu, kuma wajibi ne mu mai da hankali sosai kan wannan lamari."

Da yake ishara da cewa jami'a da Hauza suna da manufa ta musamman a fagen Mahadawiyya, sai ya tunatar da cewa: "Batun Mahadawiyya yana da zurfin ilimi don haka ya kamata hedkwatar raya al'adun Mahadawiyya ta mai da hankali na musamman kan wannan lamari."

Shugaban raya al'adun Mahadawiyya da Intizar ya yi tsokaci kan gudanar da bukukuwa daban-daban da suka hada da bukukuwan Nisfu Sha'aban da kuma ranar 9 ga watan Rabi'ul Awwal, inda ya ce: "Dole ne mu kasance da tsari guda, haduwa da hadin kai wajen gudanar da dukkan shirye-shiryen Mahadawiyya."

Ya ci gaba da cewa: "Cibiyoyin makarantun Hauza daban-daban sun sami damar gudanar da ayyukan tura masu tablig tare da hadin gwiwa da juna, kuma tare da hadafi, kuma ya wajaba hedkwatar raya al'adun Mahadawiyya da Intizar su samar da maudu'an Mahadawiyya cikin wadannan tsarukan na tablig."

Ayatullah A'arafi, yayin jaddada cewa wajibi ne wakilan kungiyoyi su rarraba ka'idojon wannan hedikwatar tare da manyan shugabannin kungiyoyin, ya bayyana cewa: "Wajibi ne a ba da fifiko kan manyan tsare-tsare na raya al'adun Mahadawiyya da Intizar a shekara mai zuwa tare da tsara su dalla-dalla da kuma aikatawa."

Da yake bayyana cewa ya kamata a baiwa matasa da dalibai fifiko a dukkan shirye-shirye, ya ce: "Batutuwa irin su Mahadawiyya da Ashura suna jawo sha'awar kasa da kasa kuma tsarin kasa da kasa kan wadannan batutuwa na da matukar muhimmanci."

Shugaban makarantun Hauza na kasar ya yi nuni da cewa, ya kamata a baiwa mata kulawa ta musamman a cikin shirye-shiryen hedkwatar domin bunkasa al'adun Mahadawiyya da Intizar, ya bayyana cewa: "Dabaru daban-daban da zasu iya taka rawa a fagen mata dole ne su kasance a wajen gudanar da ayyukan hedkwatar."

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha